Rasha ta kai hare-hare tare da lalata wani sansanin sojan sama na Ukraine a Starokostiantyniv da makamai masu linzami, a cewar ma’aikatar tsaro ta Rasha.
“Dakarun Rasha na ci gaba da kai wa cibiyoyin sojan Ukraine hari,” in ji Igor Konashenkov mai magana da yawun ma’aikatar tsaro.
“Da safiyar 6 ga watan Maris, an kai hare-hare da makamai masu linzami masu nisa. An lalata sansanin sojan Ukraine a Starokostiantyniv.”
Ya ƙara da cewa an lalata makamin S-300 na Ukraine a hare-haren.
Kazalika, Rasha ta harbe jiragen Ukraine 10 ciki har da na helikwafta cikin awa 24 da suka wuce, a cewarsa. In ji BBC.