Rundunar sojin Isra’ila a ranar Talata, ta ce, an kai hare-hare sama da 200 a cikin dare, ciki har da ma’ajiyar makamai da Hamas ke amfani da shi da kuma wasu cibiyoyi na Islamic Jihad, wata kungiyar Islama ta Falasdinu.
Daruruwan Falasdinawa masu kai hari ne suka tsallaka kan iyakar kasar zuwa Isra’ila a ranar Asabar.
Kimanin mutane 900 ne aka kashe a kisan kiyashin da ya biyo baya.
A Be’eri, wani kibbutz da ke kudancin Isra’ila, an gano gawarwaki sama da 100 a ranar Litinin bayan da sojoji suka sake kwace iko da yankin.
Mayakan Hamas sun yi garkuwa da akalla mutane 150 tare da mayar da su Gaza da suka hada da mata da kananan yara da kuma tsofaffi kamar yadda wani bincike da Isra’ila ta gudanar.
Sai dai kuma kungiyar Hamas ta yi barazanar kashe wani mutum daya da ta yi garkuwa da shi kan duk wani harin ba-ta-baci da Isra’ila ta kai kan fararen hula a Gaza.
A cewar rundunar sojin Isra’ila, ya zuwa yanzu an gano gawarwakin ‘yan ta’adda 1,500 a yankin na Isra’ila.
Hare-hare masu yawa da Isra’ila ta kai a zirin Gaza sun kashe mutane akalla 687 tare da jikkata wasu fiye da 3,800.