Gwamnatin jihar Legas ta ce, ta dawo da wasu ‘yan Najeriya 310 da suka je aikin ibada a birnin Kudus na kasar Isra’ila ta jirgin sama.
Gwamna Sanwo Olu ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata.
An kwashe ‘yan Najeriyar ne saboda rikicin da ake fama da shi a kasar Isra’ila.
Daruruwan mutane ne aka kashe a Gaza a wani harin ramuwar gayya da sojojin saman Isra’ila suka kai musu.
“Ina mai farin cikin sanar da cewa mun yi nasarar jigilar jirgin sama tare da mayar da dukkan ‘yan kasar dari uku da goma (310) da suka tafi aikin a birnin Kudus na kasar Isra’ila.
“Ina so in gode muku da damuwarku, kuma dole ne in bayyana farin cikina ga ma’aikatarmu ta cikin gida don yin aiki mai kyau.