Wani zababben dan takara a karkashin inuwar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa, wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC na jihar da suka fice daga jam’iyyar zuwa NNPP sun koyawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje darasin siyasar rayuwarsa.
Jibrin ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Politcs Today.
Jam’iyyar NNPP ta doke jam’iyyar APC mai mulki a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Ya ce, “Gwamna (Ganduje) ba ya son mu da yawa a APC. Don haka a zahiri ya tabbatar da cewa, ya kore mu daga jam’iyyar. Muka hada kanmu muka koya masa darasin siyasar rayuwarsa.
“Mun tabbatar da cewa ba zai iya numfashi a APC ba, kuma a karshen wannan rana ya sa ‘yan majalisar wakilai na APC 18, ciki har da ‘yan majalisar wakilai kusan bakwai da kasar nan ta kashe makudan kudade wajen horar da su.
“Ya haifar da ‘yan majalisar jiha 34 na APC. Zan iya gaya muku cewa wasu daga cikin waɗannan ‘yan majalisar wakilai ne masu inganci. Sun yi rashin nasara ne saboda kuri’a ce ta adawa da Ganduje.”