fidelitybank

Mun kori ɗan takarar gwamnan Jigawa – ADC

Date:

Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, ta kori dan takararta na gwamna a jihar Jigawa, Muhammad Sani Gumel, bisa zargin cin zarafin jam’iyya.

Shugaban riko na jam’iyyar a jihar Jigawa Kabiru Hussaini ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce, an kori dan takarar gwamnan ne saboda sayar da jam’iyyar ga jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Karanta Wannan: Ba mu haɗe da kowacce jam’iyya ba a Kaduna – ADC

Kabiru Hussaini ya bukaci daukacin ‘yan jam’iyyar da su marawa dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido baya.

“Muna umurtar dukkan magoya bayan jam’iyyar mu da su marawa dan takarar gwamna na PDP goyon baya domin PDP ce kadai za ta iya ceto jihar daga rugujewa baki daya,” in ji shi.

Ɗan takarar gwamnan jihar ADC Muhammad Sani Gumel ya janye takararsa ya koma APC.

Da yake mayar da martani, dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC Muhammad Sani Gumel, ya ce mukaddashin shugaban jam’iyyar ba shi da hurumin korarsa daga jam’iyyar.

Ya ce hedkwatar kasa ta kori mukaddashin shugaban jam’iyyar ne a ranar 22 ga Satumba, 2022 kuma hukumar INEC, IPAC, da hukumomin tsaro ba su amince da shi ba.

latest news 
in nigeria today 2021 punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp