Hezbollah ta ce ta yi ma sojojin Isra’ila kwanton ɓauna da daddare da abubuwa masu fashewa yayin da suke ƙoƙarin kutsawa cikin Lebanon a kan iyakar ƙasar da Isra’ila dake gabashin Lebanon.
Ƙungiyar ta kuma ce ta yi nasanar korar wasu sojojin Isra’ilar dake ƙoƙarin shiga ƙasar ta kan iyakar Yammacin Lebanon.
Isra’ila ba ta ce komai kan haka ba, sai dai ta ce an jikkata sojanta a wani gumurzu a Kudancin Lebanon a yau Laraba, an kuma jikkata wasu biyu a ranar Talata.
A jiya dai, Isra’ila ta sanar da cewa dakarunta za su shiga Yammacin Lebanon.


 

 
 