Gwamnatin jihar Kaduna, ta nuna damuwa kan cunkoson da matafiya ke fuskanta a hanyar Kaduna zuwa Abuja babban birnin tarayyar kasar.
Sanarwar da ta fitar ta ce yanzu haka suna kan tattaunawa da kamfanin Julius Berger da sauran masu ruwa da tsaki da ke aikin hanyar, don ganin an warware matsalar.
Matafiya da ke bin ta Kaduna don zuwa Abuja da sauran biranen Najeriya na cin kwakwa, kafin su iya wuce matsanancin cunkoson da ke garin Kaduna a kan titin Kaduna-Abuja.
An shafe tsawon lokaci gwamnatin Najeriya na aikin gina titin da ya tashi daga Abuja zuwa Kano, inda ya ratsa jihar Kaduna. Sai dai wasu na sukar tafiyar hawainiyar da aikin ke yi, da kuma yadda ake samun cunkoso da hatsari ga matafiya.