Hedikwatar tsaro ta bayyana a ranar Alhamis din nan cewa, a cikin kwanaki 14 da suka gabata sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 28, sun kama 113, tare da ceto 82 da aka kashe a hare-hare daban-daban a fadin kasar.
Maj Janar Edward Buba, Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan da sojoji ke yi a fadin kasar nan a Abuja, kamar yadda NAN ta ruwaito.
Buba ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun hada da ‘yan ta’adda 92, ‘yan bindiga shida, masu garkuwa da mutane uku, masu hadin gwiwa guda shida, da kuma masu satar man fetur bakwai.
A cewarsa, sojojin sun kuma kwato makamai 108 da alburusai 564, da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda 22, bindigar PKT guda shida, bindigogin fanfo guda shida, bindigogin Danish guda hudu, bindigu na kirkira, bindiga kirar Galil ace, bam na RGP guda daya. tube RPG guda daya, da gurneti 44.