Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe ‘yanbindiga fiye da 38, lokacin gumurzun da ya kai ga kian jagoran ‘yanbindigar yankin arewa maso yammacin ƙasar, Kacallah Halilu Sububu.
Cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’na na rundunar, Guruf Kaftin Kabiru Ali, ya fitar ya ce dakarun rundunar na musamman tare da haɗin gwiwar rundunar sojin ƙasa sun yi artabu da ‘yan bindigar a lokacin da suke wucewa a yankin Mayanchi.
”A lokacin gumurzun, jami’anmu sun kashe jagoransu Halilu Sububu da kuma wasu ƙarin yaransa fiye da 38”, in ji sanarwar.
Sojojin sun kuma ce sun ƙwato makamai masu yawa daga hannun ‘yanbindigar da suka haɗa da RPG biyu da RPG mai harba bam, ɗaya, bindiga ƙirar PKT uku, da AK-47 biyar da kwanson zuba alburusai 29 da kuma harsasai fiye da 1000.
Tuni dai babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa ya ce za a tura ƙarin sojoji yankin domin tabbatar da kakkaɓe sauran ‘yanbindigar da suka addabi yankin, ciki har da Bello Turji.