fidelitybank

Mun kashe wutar da ta kona ofisoshi 17 a sakatariyar Gwale – Hukumar Kashe Gobara

Date:

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da afkuwar gobarar da ta tashi a safiyar Laraba da ta kone ofisoshin sakatariyar karamar hukumar Gwale 17.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Abdullahi ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na NAN a Kano faruwar lamarin.

Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba.

“Mun samu kiran waya da misalin karfe 03:43 na safe daga Abdullahi Hassan cewa gobara ta tashi a sakatariyar Gwale.

“Bayan samun labarin, mun aika da motar kashe gobara zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 03:46 na safe domin shawo kan gobarar,” inji shi.

Abdullahi ya ce benen da aka yi amfani da shi a matsayin ofis mai tsawon mita 300 x 200 da sauransu, wanda ya kai 17, ya lalace gaba daya.

Ya kuma ce an kona motar kirar Peugeot 406, motar Hiace daya da motar daukar marasa lafiya ta tasha.

Ya kuma bada tabbacin hukumar na gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp