Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta tabbatar da tashin gobara a cikin wani gida dake Gaida Diga a yankin karamar hukumar Kumbotso.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, FSF Saminu Yusif Abdullahi ne ya tabbatar da tashin gobarar ga manema labarai a Kano.
Ya kuma ce, “Wuraren da suka kama da wutar sun haɗar da ɗakunan kwana guda uku, sai kuma ɗakin girki guda ɗaya tare da banɗaki guda ɗaya wanda suka ƙone ƙurmus”.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar, SFS Saminu Yusif Abdullahi, ya kuma gargaɗi al’umma da su ƙara kulawa.