Lokacin da muka shiga kwana na 23 da fara yakin Rasha, Ministan tsaron Ukraine ya ce kididdigarsu ta kullum da suke yi a Facebook ta nuna an kashe sojojin Rasha 14,200 daga fara yakin.
Nuna adadin wadanda aka kashen da wuraren da hakan ya faru zai zama babban kalubale, yayin da duka bangarori biyun ke ikirrarin samun nasara a kan juna.
A wani yanayi da na a saba ji ba, Rasha ta yi ikiratin an kashe sojojinta 498, amma ba ta kara cewa uffan ba kan sauran adadin.
Sai dai jami’an Amurka a ranar Alhamis sun ce, adadin wadanda suka mutu sun haura 7,000 an kuma jikkata sama da 14,000.
Cikin asarar da Rashan ta yi wadda sojin Ukraine suka yi ikirari akwai:
- Tankoki 450
- Jiragen yaki 93
- Jirage masu saukar angulu 112
BBC ba za ta iya tabbatar da wadan nan ikirarin ba.