Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladaya Amao, ya ce, an samu nasarar kashe daya daga cikin sarakunan ‘yan ta’addan, Alhaji Shanono.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ta hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet.
Ya yi alkawarin cewa, jami’an ba za su huta ba har sai an kawar da ‘yan fashi da ke addabar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a fadin kasar nan.
Babban hafsan sojin ya ba da umarnin a kara kaimi a dukkan sansanin su.
A cewarsa, hare-haren da jiragen saman NAF suka kai a yankin Arewa maso Yamma a baya-bayan nan ya nuna cewa, an kawar da ‘yan ta’adda da dama tare da lalata matsugunan su.
Ya ce, a yayin harin ta sama an kawar da wani sarkin ‘yan ta’adda, Alhaji Shanono da ke aiki a Kaduna tare da wasu ‘yan ta’adda 18, yayin da aka lalata bindigogi sama da 30 da babura 20.
Ya ce, hakazalika, an kai hare-hare ta sama a yankin Arewa maso Gabas tare da taimakon rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai, inda suka kai farmaki ta sama kan mayakan ‘yan ta’adda a Gazuwa, jihar Borno a ranar Asabar.


