‘Yan sanda a Jihar Kaduna ta sanar da kashe wasu barayin daji hudu da suka dade suna addabar mazauna garin Saminaka da ke karamar hukumar Lere ta jihar.
Tashar talabijin ta Channels ta kuma ce, ‘yan sandan sun kwace wata bindiga kirar AK47 da AK49 da aka loda wa harsasai baya ga wata motar da barayin ke amfani da ita wajen yin mummunar sana’ar tasu.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya sanar da manema labarai cewa jami’an ‘yan sandan sun yi nasarar yin arangama da barayin ne a kan babbar hanyar Saminaka zuwa Jos.
Ya ce, an gansu ne cikin wata mota kirar Sharon mai shudin launi.