Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun runduna ta daya sun kashe ‘yan bindiga uku tare da kwato makamai a Kaduna.
Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanal Kanal Musa Yahaya, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
“A bisa sahihan bayanan sirri, sojojin runduna ta daya ta sojojin Najeriya da Operation Whirl Punch sun kai wani samame a kusa da dajin Maro – Chibiya a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Nuwamba.
“A yayin farmakin, sojoji sun fatattaki ‘yan bindigar da karfin wuta, inda suka kashe daya daga cikin ‘yan bindigar tare da tilasta wa wasu tserewa da harbin bindiga zuwa dajin da ke kewaye,” in ji rundunar.
Rundunar ta kuma ce sojojin sun kama bindiga kirar AK-47 guda daya, bindigar AK-47 na gida guda daya, alburusai 7.62mm (Musamman) hudu da wayar hannu daya.
Yahaya ya kuma bayyana cewa, a ranar 10 ga watan Nuwamba, sojojin runduna da ‘Operation Whirl Punch’ a yayin da suke aikin share fage a kauyukan Kawara da Filin Jalo da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, sun tuntubi ‘yan bindiga a dajin Kawara.
“A fadan da ya barke, sojoji sun kashe dan bindiga guda daya tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya dauke da alburusai 30 na 7.62mm (Special) da babur daya da wayar fasaha daya yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga,” in ji shi.