fidelitybank

Mun karbi umarnin kotu kuma za mu bayar da tsaro a Kano – ‘Yan Sanda

Date:

Jami’an tsaro a Kano sun ce sun karbi umarnin kotu kuma za su yi amfani da shi tare da samar da cikakken tsaro a faÉ—in jihar Kano.

Cikin wani jawabin hadin gwiwa da jami’an tsaron suka gabatar wa manema labarai a shalkwatar ‘yan sanda da ke Bompai, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Usaini Gumel ya ce jami’an tsaron suna biyayya ne da umarnin da kotun tarayyar da ke Kano ta bayar.

Kotun tarayyar dai ta bayar da umarnin dakatar da soke masarautun jihar bayan shigar mata da ƙorafi kan hakan, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin fara sauraron ƙasar.

Don haka CP Gumel ya ce jami’an ‘yan sanda tare da haÉ—in gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma yi kira ga mazauna birnin Kano da su kwantar da hankula tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai, musamman yadda ya ce an san al’ummar jihar wajen bin doka da oda, kafin kotu ta yanke hukunci kan batun ranar 3 ga watan Yuni.

CP Usaini Gumel ya kuma gargaÉ—i duk wanda ya yi yunÆ™urin karya doka a jihar da cewa zai fuskanci fushin jami’an tsaro.

Yana mai cewa jami’an tsaron sun baza komarsu a faÉ—in birnin domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp