Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce ta kama kwayar Tramadol miliyan 1.1 (225mg da 100mg) a jihar Kaduna da Kano.
Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Mista Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Babafemi, ya ce an kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a cikin magungunan da aka kama a Zariya, ya kara da cewa nauyinsu ya kai kilogiram 38.3.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka, Saifullahi Sani, Salisu Nafi’u da Abdulrazaq Mamman.
A halin da ake ciki, jami’an yaki da safarar miyagun kwayoyi a filin jirgin saman Akanu Ibiam, Enugu, sun kama wani mutum mai shekaru 50, Mgbeobuna Eberechukwu, da laifin shan kwaya 77 na hodar iblis.


