fidelitybank

Mun kama ‘yan fashin Daji 6 a Zamfara ‘Yan Sanda

Date:

Dakarun ‘yan sandan Jihar Zamfara, sun kashe ɗan fashin daji tare da kama wasu shida da ake zargi da fashin da kuma satar shanu, a cewarta.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ranar Laraba, kakakin ‘yan sanda SP Mohammed Shehu ya ce dakarun sun ƙwace bindiga ƙirar AK-47 biyu, da fakitin harsasai biyu, da tarin layu, da sauransu.

A cewarsa: “A ranar 1 ga watan Janairun 2023, rundunar ta samu wani rahoton gaggawa kan ‘yan fashin daji a yankin Gusau-Magami-Dansadau. ‘Yan sanda sun isa wurin kuma suka far wa ‘yan bindigar.

“Cikin sa’a, an kashe ɗaya daga cikinsu kuma aka daƙile harinsu, suka gudu daji da raunukan bindiga.”

Haka nan, ‘yan sandan sun yi nasarar kama wani da ke da alaƙa da jagoran ‘yan fashi Halilu Kacalla mai suna Musbahu Aminu.

SP Shehu ya ce matashin mai shekara 30 ya amsa laifin aikata fashi da makami da satar shanu masu yawa a yankin.

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp