fidelitybank

Mun kama sojojin Koriya ta Arewa a Rasha – Ukraine

Date:

Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa, sojojin ƙasar Ukraine sun kama wasu sojojin Koriya ta arewa biyu da suka jikkata a matsayin fursunonin yaki a yankin Kursk na ƙasar Rasha.

Mutanen biyu suna samun kula a asibiti kuma suna hannun Hukumar Tsaro ta Ukraine (SBU) a birin Kyiv, a cewar Zelensky.

Shugaban ya ce yana godiya ga sojojin Ukraine da dakarun soji na musamman da suka kama ƴan Koriya ta Arewan.

Ya ƙara da cewa “wannan ba abu ne mai sauki ba”, yana mai cewa sojojin Rasha da Koriya ta Arewa sukan kashe ƴan Koriya ta Arewa da suka samu raunuka “don shafe duk wata shaida da ke nuna cewa Koriya ta Arewa na da hannu a yaƙin da ake yi da Ukraine”.

“Duniya na buƙatar sanin gaskiya game da abin da ke faruwa.” in ji Zelensky

Zelensky ya kuma wallafa hotunan wasu mutane biyu da suka jikkata amma bai bayar da shaidar cewa su Koriya ta Arewa ba ne.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp