Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce, ta kama wani mutum mai suna Jibrin Yusuf mai shekaru 25 da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai fyade tare da kashe ta a kauyen Kanon-Haki da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
ASP Sadiq Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
A cewarsa, mahaifin wanda aka kashen, Hassan Jibrin, a ranar 2 ga watan Agusta, 2023, ya dauki wanda ake zargin aikin jigilar taki daga daya daga cikin gonakinsa zuwa daya, dake wajen kauyen.
Da ya fahimci cewa an bar yarinyar ita kadai tana kula da takin, wanda ake zargin ya ja ta da karfi zuwa wata gona da ke kusa, inda ya yi mata fyade sannan ya yi amfani da wuka mai kaifi ya yanka mata makogwaro.
Daga nan ya kai gawar wata gona, ya rufe ta da ganye, sannan ya yi mata buhu uku na taki.
Jami’an ‘yan sandan da ke binciken lamarin sun cafke wanda ake zargin, inda rahotanni suka ce ya amsa laifin fyade da kashe yarinyar ‘yar shekara bakwai. An kuma kwato masa buhunan taki da aka sace.