fidelitybank

Mun kama mugan kwayoyi a jihohi hudu – NDLEA

Date:

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, ta ce, ta kama wasu ƙwayoyi masu yawa a jihohin ƙasar nan guda huɗu.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Femi Babafemi ya sanya wa hannu aka kuma wallafa a shafin hukumar na Tuwita, hukumar ta ce ta kama tabar wiwi da nauyinta ya kai kilo 3,975kgs da ƙwayar tramadol 58,200.

A samamen da jami’an hukumar suka kai jihohin Kaduna da Kano da Imo da kuma jihar Legas, ta ce ta kama mutum 11 da take zargi da hannu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Hukumar ta ce mutanen na amfani da dabaru da dama wajen shigar da ƙwaya zuwa Najeriya tare da yunƙurin fitar da ita zuwa ƙasashen waje irin su Birtaniya da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yaba wa jami’an hukumar a waɗannan jihohi bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen wannan kame.

Haka kuma ya yi kira ga sauran jami’an hukumar a faɗin ƙasar da su tashi tseye domin kawar da harƙallar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...

Mukarraban gwamnati ba zan lamunci dabi’ar zubar da kima ta ba – Abba

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu...

WAEC ta sake bude shafinta don duba jarabawar bana

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta bayyana...

Indonesia za ta gina asibiti dubu biyu ga Falasɗinawa

Indonesia ta sanar da cewa za ta kafa wata...
X whatsapp