Hukumar Hisbah a jihar Kano, ta ce, ta kama wata mota maƙare da kwalaben giya sama da 18,000 a ƙaramar hukumar Gwarzo da ke jihar.
Kwamandan rundunar, Sheikh Harun Sina ne ya tabbatar wa manema labaru hakan a yau Talata.
Ya bayyana cewa an kama motar ne yayin da take ƙoƙarin shiga babban birnin jihar.
Kwamnadan na Hisbah ya ce dokar da ta kafa rundunar ta haramta sha ko sayar da kayan maye a jihar.