fidelitybank

Mun kama budurwa da ta binne jariri a banɗaki – Ƴan Sandan Jigawa

Date:

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa, ta ce, jami’anta sun kama wata mata mai suna Balaraba Shehu da ke ƙauyen Tsurma a ƙaramar hukumar Kiyawa, bisa zargin binne sabon jaririn da ta haifa a ban ɗaki.

Yayin da yake tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam ya ce, sakamakon bayanan sirrin da rundunarsu ta samu ne ya kai su ga gano matar tare da tono jaririn a ban ɗakin gidan.

”Bayan haihuwar ta ne sai ta shiga ban ɗaki ta haƙa rami a kusa da masai ta binne jaririn”

Ya ce, bayan tono jaririn ne aka garzaya da shi babban asibitin Dutse inda likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu.

DSP Shiisu Adam ya ce, matar ta sanar da su cewa ta samu cikin ne ba ta hanyar aure ba, ta kuma bayyana wani saurayinta mai suna Ahmadu Sale wanda aka fi sani da ‘Dan kwairo’ da ta ce shi ne ya yi mata cikin.

Kawo yanzu dai matar mai shekara 30 tare da saurayin nata mai shekara 25 suna hannun jami’an ‘yan sanda.

Tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin mayar da batun zuwa shalkwatar cibiyar binciken manyan laifuka ta rundunar da ke babban birnin jihar Dutse.

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Cutar Mashako ta yi ajalin Yara hudu a Kano

Rahotanni na cewa cutar mashaƙo wadda aka fi sani...

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...
X whatsapp