Rasha ta ce, ta harbo jirgin yaƙin Ukraine tare da tarwatsa wasu guda uku masu saukar angulu a yankin Kharkiv.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce, dakarunta sun kai hari kan sojojin Ukraine tare da ikirarin samun nasarori.
BBC ba za ta iya tantance gaskiyar ikirarin ba. Ɓangaren Ukraine bai mayar da martani ba kawo yanzu.
Tun da farko Birtaniya ta ce, Rasha ta kasa yin komai a yankin tsawon sa’a 24, duk da ƙaruwar ayyukan dakarunta. Ta ce har yanzu Rasha ba ta karɓi ikon komai ba a ƙasa ko a ruwa.