Hezbollah ta ce ta kai wa dakarun Isra’ila hari a garin Metula da ke kan iyakar ƙasar da Lebanon a safiyar Talata.
An harba gungun makaman roka da misalin ƙarfe 08:05 (06:05 agogon Najeriya), kamar yadda wata sanarwa ta nuna, da kuma makaman atilare bayan minti 25.
Rundunar sojin Isra’ila IDF ta ce hakan ya sa na’urorin ankararwa sun yi kaɗawa, tana mai cewa an kakkaɓo wasu daga ciki, wasu sun fashe, wasu kuma “sun faɗa a fili”.
A jiya IDF ta ayyana yankunan da ke kusa da Metula, da Misgav Am, da Kfar Giladi a arewacin Isra’ila a matsayin “kullallen yankin soja”, abin da ke nufin an hana mutane shigarsa.


