Rundunar sojin Isra’ila ta ce, ɗaya daga cikin tankokin yaƙinta ta harba makami cikin kuskure kan wata tashar sintiri ta sojin Masar a kan iyakar Gaza da ke Kerem Shalom.
Kerem Shalom mahaɗar kasuwanci ce da ke rufe a yanzu a kudancin Gaza. Ita ce ta haɗa Masar da Isra’ila da kuma Zirin Gaza.
Rundunar sojin Isra’ilar ta bayyana “rashin jin daɗinta” bayan faruwar lamarin kuma ta ce tana bincike kan faruwarsa.