Sojojin Isra’ila na kai hare-hare kan wurare a Lebanon, da suka hada da tankunan yaki da manyan bindigogi, yayin da jiragenta kuma suka kai farmaki kan wani abin da ta bayyana a matsayin cibiyar ba da umarnin soji da kayayyakin aikin soji na Hezbollah.
Dakarun sojojin Isra’ila sun ce suna mayar da martani ne kan hare-haren da Æ™asar Lebanon ta kai mata a arewacin Isra’ila.
Tun lokacin da aka fara yaÆ™in, Hezbollah – Æ™ungiyar da Iran ke marawa baya wacce ke da karfin soji da siyasa a Lebanon – ta sha kai hare-hare kan wuraren Isra’ila daga kan iyaka.