Ukraine ta ce, dakarunta da suka rinka mayar da martani a kan harin da ake kai musu a kusa da birnin Kharkiv, sun isa iyakar Rasha.
Ma’aikatar harkokin tsaron Ukraine, ta wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda sojojinta da ke kan iyakoki ke kwace ikon wurare da dama da Rasha ta kwace.
Sojojin sun ce suna kan iyakar. Kazalika sojojin Ukraine sun sake kwace ikon yankuna da dama a arewa maso gabashin kasar a ‘yan kwanakin nan.
Rasha a na ta bangaren na ci gaba da lugudan wuta a yankin Donbas.