fidelitybank

Mun kafa kwamitin da zai duba hare-haren da muka kai kan fararen hula – Sojoji

Date:

Babban Hafsan Sojan Sama na kasa, Air Marshal Oladayo Amoa, ya ce, rundunar ta kafa wani kwamiti da zai tattaro bayanai kan dukkan lamuran kai hari bisa kuskure kan fararen hula da sojojin saman kasar suka yi.

A cewarsa kwamitin wanda ya kunshi manyan jami’an rundunar zai yi bitar abubuwan da suka faru har aka kai ga faruwar hakan domin daukar matakan magance su.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, Air Marshal Amao ya sanar da hakan ne a yau Alhamis, yayin da yake bude taron karawa-juna-sani kan aikace-aikacen rundunar sojin saman na shekara ta 2022 da ke gudana yanzu haka a Uyo, babban birnin jihar Akwa-Ibom.

A cewarsa manufar hakan ita ce samun shawarwari kan muhimman matakan da ya kamata a dauka domin rage yawan kashewa da raunata fararen hula a kasar yayin wasu aikace-aikacen da rundunar ta sojin sama ke yi a wasu sannan kasar.

Air Marshal Amao ya kuma kara da cewa binciken yana kuma da manufar kara tabbatar ana bin Kadin yadda sojojin rundunar ke aiwatar da umarnin da aka ba su da ba rundunar ta NAF damar koyon wasu muhimman darussan kan yadda za ta kaucewa faruwar hakan a gaba ko kuma rage irin ta’adin da irin wannan kuskure ke yi.

Kazalika da kuma daukar karin matakai don rage cutar da fararen da ke zaune a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.

Yayin da yake taya sabbin matasan matukan jiragen yaʙi 17 da aka yaye a wajen taron, Mista Amao ya hore da su bi ka’idojin aiki da aka shimfida a yayin da suke fagen daga, kana su dauki dukkan matakan da suka wajaba wajen kare fararen hula da kuma rage illata su.

Sai dai sanarwar, wadda mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar ba ta sanar da lokacin da ake tsammanin kammala wannan binciken da fitar da sakamako ba.

Mutuwa da kuma raunata fararen-hula a cikin hare-haren sojojin sama a Najeriya abu ne da ke ta maimaituwa a shekarun bayan bayan nan, tun bayan sakin wani bam bisa kuskure da suka yi a garin Rann na jihar Borno wannan ya yi sanadin mutuwar ā€˜yan gudun hijira da ma’aikatan agaji fiye da dari daya shekaru biyar da suka wuce.

Ko a watan Satumban bara ma fararen hula fiye da 10 ne suka rasa rayukansu a kauyen Buhari na jihar Yobe wasu kuma 20 suka samu raunuka a wani harin da wani jirgin saman soji ya kai musu bisa kuskure.

Lamarin dai bai tsaya kan fararen hula ba kadai domin wasu sojoji da dama sun rasa rayukansu a wata Afrilun barar lokacin da wani jirgin yaʙi ya kai wa motar su hari bisa kuskure a yankin Mainok na jihar Borno bayan da sojojin na kasa suka kira a kawo musu dauki a arangamar da suke yi da mayakan Boko Haram a lokacin.

Akwai lamurra makamantan haka da suka faru a wasu yankuna cikin har da jihar Zamfara inda sojojin ke fada da ā€˜yan fashin daji.

legitnewsnigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp