Babban Jami’in Shakhtar Donetsk, Shugaba, Serhiy Palkin, ya bayyana irin gargadin da ya yi wa Chelsea a lokacin da suke kokarin sayen Mykhailo Mudryk daga kulob din na Ukraine a lokacin bazara.
Palkin ya ce bai yi nadama ba game da komawar dan wasan zuwa Stamford Bridge kuma ya nace cewa kuma babu mamaki kan yadda ya fara rashin nasara a gasar Premier.
An ce dan wasan mai shekaru 22 yana kan hanyarsa ta zuwa Arsenal amma Chelsea ta share ta kuma cimma yarjejeniya ta sama da fam miliyan tamanin da tara.
Mudryk bai yi wani tasiri ba a wasanni tara da ya buga wa Blues kuma Palkin ya bayyana cewa ya hadu da Mudryk a makon da ya gabata kuma ya tabbatar da cewa dan wasan ya ci gaba da kasancewa cikin farin ciki.
Ya shaida wa Sky Sports cewa: “Mako daya da ya wuce a Ingila na hadu da Mykhailo Mudryk kuma ya yi farin ciki matuka.
“Na ce tun farko, na yi magana da masu Chelsea, kuma na gaya musu cewa kuna da lu’u-lu’u na gaske, amma ya kamata ku yi hakuri da gaske. Ku ba wa wannan mutumin lokaci kuma zai nuna muku abin da zai iya kawowa kulob din.”