Bayanai game da binciken da FBI ta gudanar a gidan tsohon shugaban Amurka Donald Trump ranar Litinin a Florida sun nuna cewa hukumar ta gano wasu takardu har kashi 11, wasunsu kuma dauke da bayanan tsantsar sirri na kasar.
Bayanan sun ce makasudin samamen na FBI shi ne kan zargin da ake wa Trump din da karya dokokin leken asiri na Amurka, wanda ya shafi ajiye takardu masu matukar muhimmanci ga kasa.
Wadanda ya kamata su kasance a wata ma’ajiya da ke karkashin gwamnati ita kadai.
Wakiliyar BBC ta ce FBI ta je Mar a Logo gidan tsohon shugaba Donald Trump, inda ta bincike dakuna kwana 58, da ban-daki 33.
Wani alkalin Amurka ne ya fallasa bayanan da ke kunshe a takardar, bayan da tsohon shugaban kasar ya ce ba zai hana a fitar da bayanan ba.
A martaninsa ta shafinsa na sada zumunta, Donald Trump ya ce, ya ajiye takardun ne a wata ma’ajiya mai tsaro, kuma a cewarsa zai iya mika su ga hukumar inda sun bukata cikin lalama, ba sai sun sanya siyasa cikin lamarin ta hanyar kai samame a gidansa ba. In ji BBC.


