Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ya c,e gwamnatin Najeriya ta gano mutum 100 masu taimaka wa ƙungiyar Boko Haram da kuɗaɗen da take tafiyar da ayyukanta.
Ya kuma ce mutanen suna da alaƙa da aƙalla ƙasashe goma.
Aregbesola wanda ya bayyana haka a ranar Lahadi ya ce yanzu haka gwamnati ta kama mutum 48 cikin 100, wadanda Ɓangaren tattara bayanan sirri na hada-hadar kuɗin ƙasar ya ambato.
Kuma a cewarsa tuni aka fara tuhumar wasu daga cikin su.
A cikin shekarun da suka gabata dai gwamnatin Najeriya ta ce tana ƙoƙari wajen damƙe mutanen da ake zargin su da tallafa wa ta’addanci.
A watan Maris ɗin 2021,gwamnatin ƙasar ta ce ta kama masu sana’ar canjin kuɗi a ƙasar sama da 400, waɗanda ake zargi suna da hannu wajen tura wa ƙungiyar Boko Haram kuɗi.