Dakarun sojin ƙasa sun ce, sun gano tare da lalata wata masana’antar da ake ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba a unguwar Vom da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau da ke tsakiyar Najeriya.
Cikin wani saƙo da rundunar sojin ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce ta gano bindigogi masu yawa a lokacin samamen.
Daga cikin bindigogin da sojojin suka gano a masana’atar akwai ƙirar AK-47 shida, da ƙananan bindigogi masu sarrafa kansu guda huɗu da jakankunan AK 11 da ƙaramar bindiga ƙirar Pistol.

Sauran abubuwan da sojojin suka ce sun gano, sun haɗar da kwanson saka alburusai na AK-47 huɗu, da sauran kayyakin ƙera bindigogi daban-daban.
Haka kuma sanarwar ta ce sojojin sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a gudanar da masana’antar.