Shugaban kungiyar sa ido kan zaɓen Najeriya ta Commonwealth, Thabo Mbaki, ya buƙaci dukkan masu zaɓe da su fito su zaɓi waɗanda suke so domin shugabantar su.
Thabo Mbeki wanda ya kasance tsohon shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, ya bayyana haka ne lokacin da masu sa ido na kungiyar suka ziyarci wasu rumfunan zaɓe a Abuja babban birnin Najeriya.
Kungiyar ta ƙasashe renon Ingila na sa ido ne a daidai lokacin da miliyoyin ‘yan Najeriya suka fita rumfunan zaɓe daban-daban da ke faɗin ƙasar domin zaɓan shugaban ƙasa da kuma ‘yan majalisar dattawa da kuma wakilai.