fidelitybank

Mun fatattaki Ƴan Bindiga a Katsina – Dakarun Haɗin Gwiwa

Date:

Dakarun haɗin gwiwa na jami’an tsaron Najeriya da ke aikin soji na musamman wato Operation Fansan Yamma, sun ce sun samu nasarar fatattakar ƴanbindiga daga yankin Tudun Bichi da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar Katsina.

A wata sanarwa da Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce sun samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukan ƴanbindigar a yankin.

Ya ce, “a farmakin haɗin gwiwa da dakarunmu suka kai, bayan jirgin sama ya tarwatsa su, sai suka sake haɗuwa a wani gefen, inda nan kuma sojojin ƙasa suka gwabza da su, kafin suka arce.

Ya ce jirgin sama ya bi su a baya yana buɗe musu wuta, inda ya ce ƴan ƙauyukan yankin sun tabbatar musu da mutuwar wasu daga cikin ƴanbindigar, tare da raunata wasu manyan ƴanbindiga irin su Manore da Dpogo Nahalle.

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp