Hukumomi a Jihar Borno, sun ce sun fara rasa wuraren da za su ajiye mayaƙan Boko Haram da suka miƙa wuya.
Babban jami’in soja Manjo Janar Chris Musa ya ce a yayin da miƙa wuyan da mayaƙan Boko Haram ɗin ke yi yake taimakawa wajen shawo kan rikicin da ya addabi yankin, a gefe guda kuma babu isassun wuraren ajiye su.
Babban janar ɗin ya ce zuwa yanzu akwai mayaƙan da suka yi saranda kuma suke jiran bin matakan sauya musu tunani, amma ba su da wajen ajiye su.
Wuraren ajiye mutanen sun cika maƙil – kuma a yanzu hukumomi suna duba yiwuwar gina wasu.
Matakan sauyawa da gyara tunani na cikin ƙoƙarin da gwamnatin Najeriya ke yi don kawo ƙarshen ayyukan masu iƙirarin jihadi, musamman a arewa maso gabashin ƙasar. In ji BBC.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa kusan mutum 350,000 ne suka mutu a rikici tsakanin ƙungiyar Boko Haram da rundunar sojin ƙasar cikin shekara 12. Amma adadin ka iya fin haka.
Janar Chris Musa ya ce, wani babban ƙalubalen shi ne yadda suke samun matsalar mayar da ƴan gudun hijira matsugunansu.
Hakan na faruwa ne sakamakon ƴan tayar da ƙayar bayan sun daddasa nakiyoyi a kan hanya.