fidelitybank

Mun fara bincike akan Askarawan mu da ake zargi da wuce gona da iri – Zamfara

Date:

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce, tana gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Askarawan jihar cewa, suna wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaro a yankunan jihar.

Wannan na zuwa ne bayan zargin da wasu mazauna Tsafe suka yi cewa, Askarawan sun kama tare da kashe musu ‘yan uwa a lokacin da suke tsare da su.

Ƴan uwan waɗanda abin ya shafa sun zargi Askarawan da ke aiki a karamar hukumar Tsafe da kashe wani matashi mai suna Hamza bayan kama shi.

“Wani kaninmu ya tafi gona nan Tsafe, dama bisashe na masa É“arna kullum yana can yana tsare gonar tasa. Ranar sai ya faÉ—a wa mai bisashen cewa idan suka sake masa É“arna zai kai su ga huÆ™uma,” in ji É—an uwan mamacin.

Ya ce matan da ya kai karar wurinsu a ce matan ƴan askarawan ne, inda matan suka kira mazajensu suka ce matashin na musu ɓarazana.

“Daga nan ne suka zo suka kama shi su ka je da shi ofis É—in su suka riÆ™a dukansa, jini yana fita ta kunnesa,” in ji É—an uwan.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun faruwar irin haka da ya shafi askarawa a yankin Tsafe ba, inda ko a kwanan baya an samu wani al’amari da ya shafi wani magidanci da ake zargin ya rasa ransa lokacin da yake tsare a hannun askarawan.

Mazauna yankin sun buƙaci hukumomin Zamfara da su yi wa mamatan adalci ta hanyar ɗaukar mataki akan waɗanda ake zargi ta hanyar hukunta su idan aka same su da laifi.

Sai dai gwamnatin jihar ta Zamfara ta shaida wa BBC cewa ba ta da matsaniya kan al’amarin, amma a shirye take domin gudanar da bincike.

nnnhausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp