Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce, ta fara gudanar da bincike kan zargin kashe wani sifeton ‘yan sanda da wasu jami’an sojin ruwa suka yi a yankin Okokomaiko da ke Ojo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa NAN haka a ranar Lahadi.
Hundeyin ya ce an samu rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sanda na Okokomaiko da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Asabar daga wasu jama’a.
Ya ce rahoton ya nuna cewa wasu ‘yan sanda da ke sintiri na yau da kullum a kan yankin Igbo-Elerin, sun yi kokarin damke wani babur da ke kan hanya a tashar Beno.
Kakakin ya ce wasu mutane biyu da ke kan babur din, wadanda ke sanye da mufti, wadanda suka ce jami’an sojin ruwa ne, sun yi turjiya da kama su, suka far wa ‘yan sandan.
“Sauran jami’an sojan ruwa sanye da kakinsu sun isa wurin inda suka goyi bayan abokan aikinsu a harin.
“A lokacin da wani Sufeto ya fado ya sume, sai jami’an Sojin ruwa suka tsere daga wurin.
“An ceto sufeton kuma an garzaya da shi asibiti a yankin, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
“An ajiye gawar a dakin ajiye gawa na Idi-Araba, Yaba, domin a tantance gawarwakin, yayin da ake ci gaba da bincike,” in ji shi.