Rasha ta ce ta lalata jirage marasa matukan Ukraine da dama waɗanda suka yi ƙoƙarin kai mata hari a yammacin ƙasarta.
Sanarwar Rashan ta zo ne kwana guda bayan ta kai harin makamai masu linzamin a kan wani ƙauyen Ukraine da ya yi sanadin rasa rayukan mutum fiye da 50.
Ƙasashen duniya dai na ta Alla-wadai da wannan hari da Rashan ta kai.
Yawancin waɗanda suka mutu sakamakon harin a ƙauyen na halartar jana’iza ne.
Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana harin a matsayin mai tada hankali.
Shi ma Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, ya ce wannan ya nuna irin rashin imanin Rasha.
Hroza dai na cikin yankin Kharkiv da ke gabashin Ukraine.