Gabanin zaben 2023 mai gabatowa, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta koka da yadda a yanzu ‘yan siyasa ke sayen katin zabe na dindindin, PVC, domin yin magudi tare da bata sahihancin aikin.
Wannan bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da masu kada kuri’a a fadin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar nan suka fito domin karbar katin zabe. Wannan tsari ya fara ne a ranar 12 ga Disamba kuma ana sa ran zai ƙare a ranar 27 ga Janairu 2023.
Mukaddashin shugaban hukumar zabe ta INEC kuma kwamishinan kasa mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Nasarawa, Kaduna da Filato Mohammed Haruna ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin kaddamar da shirin #VoteMatters na wata kungiyar sa ido kan zabe mai suna NESSACTION a Abuja.
Haruna ya bayyana cewa, a kwanakin baya ne Hukumar ta kama wasu mutane biyu a jihohin Sokoto da Kano bisa laifin mallakar PVC ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma jaddada cewa a yanzu ‘yan siyasa suna sayen katin zabe, inda ya gargadi masu kada kuri’a da kada su sayar da katinsu saboda kowane dalili, saboda laifi ne da za a hukunta su.
Ya ce, “Wasu daga cikin ku na sane da cewa a baya-bayan nan ne INEC ta yi nasarar hukunta wasu mutane biyu da aka samu da laifin mallakar PVC ba bisa ka’ida ba a Kano da Sakkwato. Don haka ina kira ga jama’a da su tattara PVCs din su, su kiyaye su, sannan su tabbatar kun fita can ku kada kuri’u a ranar zabe domin ba za ku iya kada kuri’a ba tare da PVC din ku ba.”