Kungiyar matasan Arewa ta nuna damuwar ta a kan rashin jituwar da ke tsakanin masarautar Kano da kamfanin Air Peace.
Kungiyar ta yi kira ga manyan ‘yan Najeriya da su shiga lamarin kan wannan dambarwar.
Shugaban kungiyar Alhaji Yerima Shettima ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, abun damuwa ne yadda a ka gaza magance rashin jituwar da ke gudana a yanzu, saboda dattawan kasar sun ki mayar da hankali kan haka ko kuma su yi wani yunkurin, domin ganin an samu zaman lafiya.
Mun ji cewa Yarima Isa Bayero, shugaban tsare-tsare na Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zargi kamfanin jirgin da wulakan ta sarkin ta hanyar kin jinkirta tashin jirginsa na Lagas zuwa Kano, bayan ya jinkirta tashinsa daga Banjul, kasar Gambia zuwa Lagas.
Sai dai kamfanin jirgin ya karya ta batun wulakanta sarkin sannan ya ce, ya gwammace ya kare martabarsa ta hanyar kin jinkirta tashi wanda an riga an kammala tsare-tsare.
Isa Bayero ya kuma baiwa kamfanin awanni 72 ya bayar da hakuri ga sarkin da mutanen masarautar tun a ranar Asabar.