Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce jamiāanta sun kama wani da ake zargin manomin tabar wiwi irin ta kasar Indiya a jihar Sokoto.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Mista Adamu Iro, ya shaida wa manema labarai ranar Asabar cewa “Wannan shi ne karo na farko da aka samu irin wannan lamari a tarihin jihar”.
A cewar Iro, wanda ake zargin, Anas Sani, an kama shi ne a kauyen Sayinna da ke karamar hukumar Tambuwal, bayan da aka samu labari.
Ya ce wanda ake zargin ya shuka nauāin tabar wiwi na kasar waje a cikin gonarsa ta masara, wadda jamiāan NDLEA suka tayar da su suka mamaye gonar.
Kwamandan ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin bayan binciken dakin gwaje-gwaje na ganyen da aka tumbuke.
Ya godewa mazauna yankin bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar, ya kuma bukace su da kada su yi kasa a gwiwa, yana mai gargadin cewa noman hemp na Indiya da muāamala da miyagun kwayoyi na jawo hukunci mai tsanani.


