fidelitybank

Mun dakile mumunan harin da aka yi kokarin kaiwa Kano – Irabor

Date:

Jami’an tsaro sun daƙile wani yunƙurin kai hari a Jihar Kano, wanda ka iya zama mafi muni a ƙasar nan, a cewar Babban Hafsan Tsaro na kasa, Janar Lucky Irabor.

Janar Irabor ya bayyana hakan ne a yau Lahadi yayin da ya bayyana cikin wani shiri kan Ranar Dimokuraɗiyya a kafar talabijin ta Channels TV.

Ya ce, an daƙile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari kan wata coci a garin Owo na Jihar Ondo, wanda ‘yan bindiga suka buɗe wa masu ibada wuta tare da kashe mutum fiye da 40.

“Babu mamaki ba ku da labari cewa a makon da ya wuce kaɗai da aka kai harin coci a Owo, a Kano misali, mun yi nasarar daƙile harin da ka iya zama mafi muni a ƙasar nan tamu saboda bayanan sirri da muka samu,” in ji shi.

“A wannan aikin, mun gano kayayyakin da ake haɗa abubuwan fashewa da su. Mun ƙwace ƙunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ƙoƙarin yin amfani da su a sassan ƙasa, har da Abuja.”

Janar ɗin ya ƙara da cewa harin Owo da aka kai ba ya nuna cewa ba a samun ci gaba a faɗin Najeriya ba, yana mai cewa “harkokin tsaro sun inganta a shekara ɗaya da ta wuce”.

daily post nigeria today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp