Hedikwatar tsaro ta tabbatar da cewa dakarun runduna ta 29 Task Force Brigade, sun dakile wani hari da wasu ‘yan ta’adda suka kai wa ayarin motocin Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ranar Asabar.
Wata sanarwa da Daraktan Ayyuka na Yada Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, a ranar Litinin a Abuja, ya ce sojojin sun kuma kwato motoci biyu da lamarin ya shafa.
Ya ce direban babbar motar soji daya, ‘yan sanda hudu da jami’an DSS daya da suka samu raunuka a harin na cikin koshin lafiya.
A cewarsa, daya daga cikin ‘yan sandan da suka rakata ya mutu ne jim kadan da isar su asibitin kwararru na Damaturu.
“Rundunar sojojin ta 29 Task Force Brigade karkashin jagorancin kwamandan birgediya suna gudanar da sintiri na yaki a yankin domin gano ‘yan ta’addan da suka aikata wannan aika aika.
“Motoci biyu da lamarin ya shafa sun hada da, MRAP na soji daya da kuma wata motar rakiyar farar hula daya da aka harba tayoyinsu a lokacin da lamarin ya faru, an kwato su cikin koshin lafiya zuwa sansanin sojoji da ke Benisheikh.
“Ana ci gaba da gudanar da ayyukan farauta tare da lalata ‘yan ta’addar da suka kai harin,” in ji shi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa ‘yan ta’adda sun yi wa ayarin motocin gwamnan kwanton bauna a lokacin da suke komawa Damaturu daga Maiduguri, kimanin kilomita 6 daga garin Benesheikh a ranar Asabar.
Gwamnan ba ya cikin ayarin motocin a lokacin da aka yi musu kwanton bauna.
Sakataren gwamnatin jihar da wasu manyan jami’an gwamnatin da ke cikin ayarin ba su ji rauni ba.