Hukumar da ke kula da aikin ‘yan sanda (PSC) ta dakatar da aikin daukar sabbin jami’an ‘yan sandan Najeriya na kwansitabil.
Hukumar ta yi hakan ne kasa da sa’o’i 24 da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya fusata kan wata tallata daukar aiki.
IGP, Hukumar Kula da Sabis ta ‘Yan Sanda a sabon rikici kan daukar ma’aikata
Bayan rahoton Aminiya, ‘yan sanda sun sake gurfanar da direban da ya murkushe dalibar
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, IGP ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da tallan da aka sanya a cikin jaridun kasar.
Da take mayar da martani a ranar Talata, hukumar a cikin wata sanarwa da kakakinta, Ikechukwu Ani, ya fitar ta tabbatar da cewa akwai batutuwa tsakanin rundunar ‘yan sanda da hukumar, inda ta ce za a daidaita al’amura cikin gaggawa.
Ya roki ‘yan Najeriya da suka nuna sha’awar shiga aikin rundunar da kada su nemi aikin har yanzu domin baiwa hukumar lokaci ta sasanta rikicin da ke tsakaninta da hukumomin ‘yan sanda.
Ani ya ce: “Hukumar ‘yan sanda ta lura da yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta buga game da aikin daukar ma’aikata na 2022. ‘Hukumar na son bayyana cewa, za a warware duk wasu batutuwan da suka shafi wannan aiki a tsakanin bangarorin biyu domin maslahar kasa.
“Duk masu sha’awar neman aiki da sauran ‘yan Najeriya masu son yin aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya su yi hakuri yayin da ake magance wadannan matsalolin.
“Hukumar za ta ci gaba da kokarin baiwa ‘yan Najeriya ‘yan sandan da za su yi alfahari da su.”
Aminiya ta tuna cewa a baya Hukumar PSC ta kai karar Hukumar NPF da kuma tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu, bisa laifin gudanar da aikin daukar ‘yan sanda 10,000 a shekarar 2019, amma daga baya aka shawo kan lamarin.
Rashin jituwar da aka samu a wancan lokacin shine ko alhakin hukumar PSC ko NPF ne ta tafiyar da tsarin daukar ma’aikata.


