Jami’an tsaron farar hula da ba da agaji na Civil Defense, sun ce sun daƙile shirin da wasu matasa suka yi na gudanar da abin da ta ce auren ‘yan luwadi ne a jihar Gombe.
Rundunar ta bayyana cewa jami’anta sun kama matasa kimanin 76 waɗanda suka taru a harabar wata kasuwar zamani da ake kira Duwa Plaza domin gudanar da bikin.
Kwamandan hukumar a Gombe, Mohammed Muazu, ya faɗa wa BBC Hausa cewa sun haɗa taron murnar zagayowar ranar haihuwa ne tukunna, inda za su yi bikin auren daga baya.
Ya ƙara da cewa babu wanda ya kai shekara 25 a cikin matasan. Sai dai bai yi bayani ba ko dukkansu maza ne.


