Shugaba Vladmir Putin ya sanar da haramtaccen kwace kan yankuna guda hudu na kasar Ukraine, inda ya ce a yanzu sun zama mallakar Rasha.
A wani jawabi da ya gabatar cikin fushi yana kokawa da halayyar kasashen Yamma, Putin ya yi ikirarin cewa mutanen da ke zaune a yankunan ne suka zabi komawa cikin kasar Rasha.
Sai dai an bayyana “kuri’ar raba gardamar” da aka gudanar a matsayin wani buge kawai.
Yankunan da Rasha ta kwace su ne Donetsk da Luhansk da Kherson da kuma Zaporizhzhia. Sai nan da ‘yan kwanaki ne za a yi bikin hade yankunan cikin Tarayyar Rasha a hukumance. In ji BBC.