fidelitybank

Mun cimma matsaya a kan sabon albashin ma’aikata – Gwamna Uzodimma

Date:

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce, kwamitin tsara mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Najeriya ya kusa cimma matsaya a kan sabon albashin.

A ƙarshen taron kwamitin, gwamna Uzodimma, ya ce bayan shafe sa’oi 12 ana tattaunawa tsakanin mabobin kwamitin, an cimma matsaya kan shawarar da ta dace su bai wa gwamnati.

Gidan talabijin ɗin Channels ya ruwaito gwamna Uzodimma, ya na cewa: “Mun yi tattauwa mai daɗin gaske kuma ana iya cewa mun cimma matsaya a matakinmu na ƙaramin kwamitim, domin haka idan muka je ga babban kwamiti komai zai tafi lafiya.”

Ya yi bayanin cewa kwamitin ya tuntuɓi duk waɗanda ya kamata, kuma sakamakon rahoton sa zai zamo abin da ake sa ran yin amfani da shi wajen cimma matsaya a babban kwamitin da zai yi aiki na gaba a kan sabon albashin.

Gamayyar kungiyoyin ƙwadago a Najeriya dai ta ƙi amincewa da tayin naira 60,0000 da gwamnati ta yi mata a matsayin mafi ƙarancin albashi, lamarin da ya sa ta fara yajin aikin gama gari daga ranar Litinin.

Sai dai gamayayar ta dakatar da yajin aikin a ranar Talata bayan gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin ƙara wa a kan tayin ta na farko, kuma hakan ya buɗe sabuwar hanyar tattaunawa a kan batun.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp