fidelitybank

Mun ceto mutum 63 da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna – Nuhu Ribadu

Date:

Gwamnatin Najeriya ta miƙa wa gwamnatin jihar Kaduna mutum 63 da ta ce ta kuɓutar daga hannun ‘yan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar ta Kaduna.

Gwamnatin ta miƙa mutanen ne ta hannun ofishin mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, bayan kula da lafiyarsu da aka yi a asibiti na tsawon kwana biyu.

Mutanen da aka ceto daga hannun ‘yan bindigar su 63 waɗanda suka haɗa da mata 24 da maza 39 an kama su ne a ƙaramar hukumar Ɗan-Musa ta jihar Katsina a hare-hare daban-daban – mafi yawan shekarunsu shi ne Malam Ibrahim Audu mai shekara 65, mafi ƙanƙantarsu kuuwa shi ne wani jariri mai ƙasa da shekara ɗaya wanda aka kama mahaifiyarsa wata uku baya.

Babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa ya ce aikin haɗin kai da suke yi tsakanin gwamnatoci da mutanen gari da suke bayar da bayanai shi ya kai ga samun nasarar kuɓutar da waɗannan mutane.

“shugaban ƙasa da ofishin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro suna ba mu gudunmuwar da ta kamata wajen aikinmu. In ka ga mutanen da aka kama sai ka yi mamakin mai ya sa mutane za su kama su? Domin babu wani abu da za a samu a hannunsu. Mutane ne da ke neman abin sawa a baka.

“Muna so mu gaya wa ‘yan ƙasa muna aiki ba dare ba rana domin tsare su. Ba mu biya ko sisi ba aka sake su. Sai da aka kai su asibiti aka duba lafiyarsu waɗanda ba su da lafiya aka ba su magani aka kuma ba su abinci da sutura suka sa,” in ji Janar Christopher Musa.

Sani Liman Kila shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Kaduna wanda ya karbi mutanen a madadin gwamnan jihar Sanata Uba Sani – ya ce ba kodayaushe ne ake buƙatar yaƙi da ‘yanbindiga ba domin kuwa a lokuta da dama sulhu na taka muhimmiyar rawa wajen ceto mutanen da ake garkuwa da su.

“Dole mu yi godiya ga shugaban ƙasa da NSA, kuma a madadin gwamnan jihar Kaduna za mu ci gaba da bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro.

“Babu shakka a sakamakon sulhun da aka yi ne da ‘yan bindigar suka sako mana waɗannan mutane, da sulhu ba ya aiki da ba a yi haka ba,” in ji Kila.

Sadi Adamu ɗaya ne daga cikin waɗanda aka kama, kuma ya shafe shekara ɗaya da wata biyu a hannun ‘yan bindigar.

“Na gode wa Allah da kuma gwamnati, wallahi ba ma cin komai sai masara ɗanya da totuwarta. Ni har na haƙura da iyalaina na ce su koma gida amma yanzu na ce su dawo,” in ji Sadi.

A nata ɓangaren Shafa’atu Idris ta ce ta kwashe makonni 11 a hannun ‘yanbindigar.

“Randa suka kama ni a cikin jini na tsallake mijina na bar shi. Sun tafi da ni da ɗana. Abin takaicin shi ne sai su tambaye ka kuɗin fansar da watakila kai da danginku baki ɗaya ba ku da shi. Amma na yi godiya ga gwamnatin Najeriya,” in ji Shafa’atu.

Akwai mutane da dama irin waɗannan da har yanzu suke hannun ‘yanbindiga a sassa daban-daban a Najeriya, sai dai gwamnati na jaddada alƙawarin ba za ta huta ba har sai ta ga yadda za ta kuɓutar da su, ta sake haɗa su da iyalansu, wani abu da ke zama ƙwarin gwiwa ga waɗanda suke tsaren.

Matsalar tsaro a Najeriya na neman zama irin abin da ‘yan magana ke cewa ana maganin ƙaba kai na ƙara kumburi – yayin da gwamnati ke cewa tana samun nasara a yankuna irin na su Birnin Gwari a can jihohin Sokoto da Kebbi kuma an samu ɓullar wata ƙungiya da ake kira Lakurawa. Kodayake gwamnati ta ce ba za ta huta ba har sai ta kawo ƙarshen wannan ƙungiya.

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp