Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, reshen jihar Benin, sun cafke wasu mutane shida da ake zargi da damfarar yanar gizo a garin Benin na jihar Edo.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a.
Hukumar ta bayyana sunayen wadanda ake zargin, Thomas Osigbemen, Kennedy Uwuigbe, Osameda Osazee, Enofe Macaulay, Wilfred Ikhireagie da Osayande Prosper.
An kama su ne a maboyarsu, bisa samun bayanan sirri da ake zarginsu da aikatawa.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyi, kwamfutar tafi-da-gidanka da motoci, 2 Lexus RX350, 2 Lexus E5 330, Mercedes Benz GLK 350, Mercedes Benz CLA 250, Toyota 4 Runner, Toyota Corolla da Toyota Avensis.
Hukumar ta EFCC, ta kara da cewa, wadanda ake zargin sun yi maganganu masu amfani kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu.


